(ABNA24.com) Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Seyyed Abbas Moussavi, ya ce zaben Aljeriya babban ci gaba ne ta fuskar demokuradiyya.
Mista Moussavi, ya kuma yi fatan hakan zai bude wani sabon babi tsakanin jamhuriya musulinci ta Iran da kuma Aljeriya.
A ranar Juma’a data gabata ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Aljeriya, ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar na ranar 12 ga watan Disamba, wanda ya bayyana dan takara Abdelmadjid Tebboune, ya yi nasara da kasha 58,15% na yawan kuri’un da aka kada.
/129
16 Disamba 2019 - 06:11
Lambar labari: 994127
Iran ta yaba wa kasar Aljeriya akan yadda ta shirya zaben shugaban kasa mai kyau.